Zaɓe cikin gardama a Burundi | Labarai | DW | 21.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓe cikin gardama a Burundi

An buɗe runfuna zaɓe a Burundi a zaɓen shugaban ƙasar da ke gudana a yau cikin rikici.Wanda'yan adawar suka ƙaurace masa kann cewar za saɓama doka.

'Yan adawar ƙasar sun ce zaɓen bai halarta ba,saboda takarar shugaba Pierre Nkuriziza a waadi na uku, ta saɓama kudin tsarin mulkin ƙasar.

Tun da farko Cocin Roman Katolika na ƙasar ta janye daga lura da saka ido a kan al'amuran zaɓen saboda rashin sahihancinsa.

A jiya a cikin dare an ji ƙaran wasu abubuwan da suka fashe tare da jin ɗuriyar harbe-harbe wanda aka ci gaba da yin harbe-harben.Wasu rahotannin da ke zo mana sun ce mutane biyu sun mutu ɗaya ɗan sanda da wani farar hula.