Zaɓe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da rikici | Labarai | DW | 14.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da rikici

'Yan takara biyu ne watau Anicet George Dologuele da Faustin Archange Touadera ke fafatwa a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokoki.

A zagaye na farko na zaɓen shugaban ƙasar da aka yi Anicet Dologuele shi ne ke kan gaba da kishi 24 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa yayin da Faustin Touadera ke da kishi 19 da 'yan kai cikin 100.
Ƙasar ta jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta faɗa cikin wani tashin hankali na rikicin addini tsakanin musulmi da kirista a shekarar 2013, bayan da ƙungiyar Seleka ta musulmi ta ƙwaci iko daga hannu François Bozizé, abin da ya janyo asarar rayukan jama'a da dama.