Zaɓen Majalisar Dokoki a jihar NRW
May 9, 2010Tun kafin zaben na majalisar dokokin jihar Northrhine Westfalia a ranar Lahadi, aka ga alamun cewar masu kada kuri'u zasu nuna rashin goyon bayan su ga aiyukan da gwmanatin da tayi mulki har ya zuwa wannan lokaci, wato karkashin Pirimiya Jürgen Rüttgers na jam'iyar CDU da Pinkwart na jam'iyar FDP. Sakamakon da aka samu daga zaben ya nunar da cewar masu zabe sun kada kuri'ar rashin goyon baya ga wannan gwamnati, inda jam'iya mafi girma a wannan hadin gwiwa, wato CDU, tayi asarar akalla kashi goma da rabi cikin dari na kuri'u, idan aka kwatanta da shekaru hudu da suka wuce. A zaben na jranar Lahadi, jam'iyar ta CDU ta sami abin da bai wuce kashi talatin da hudu da digo hudu cikin dari ba, idan aka kwatanta da misalin kashi arba'in da digo shidda da ta samu shekaru hudu da suka wuce. Dangane da haka, Pirimiyan jihar ta Northrhine Werstfalia, kuma shugaban jam'iyar CDU a jihar, Jürgen Rüttgers yace ya dauki alhakin duk irin kayen da jam'iyar tasha a zaben na jihar Northrhine Westfalia.
Yace wannan zabe na yau ya zama mummunan abu ga jihar Northrhine Westfalia da kuma gareni musamman. Sakamakon da aka samu ya zama na bakin ciki , musamman saboda mun gudanar da kampe ne tare da imanin cewar mun gudanar da kyakkyawan aiki tsawon shekaru biyar na mulkin mu ga al'ummar jihar Northrhine Westfalia.
Zaben majalisar dokoki a wannan jiha, da ita ce tafi yawan jama'a a tsakanin jihohi goma sha shida na Jamus baki daya, ya dauki hankali, musmman ganin cewar sakamakon da aka samu, zai zama mai muhimanci ga tsarin aiyukan mulki a kasa baki daya, musamman a gwmnatin taraiya da aiyukan ta a babbar majalisar dokoki ta Bundesrat. Shugaban jam'iyar adawa ta Social Democrats wato SPD a majalisar dokoki ta jihar, Hannelore Kraft dake jawabi gaban dimbin magoya bayan ta, tace:
Yanzu dai ya tabbata masu zabe sun kawar da gwamnatin hadin gwiwa ta CDU da FDP. Sakon da muke dauke dashi daga jihar Northrhine Westfalia shine: yanzu dai jam'iyar SPD, ta farfado inda aka santa a da.
To sai dai kuma ko da shike jam'iyun CDU da FDP ba zasu sami damar ci gabada aiyukan mulki na jihar ta Northrhine Westfalia bayan zaben na ranar Lahadi ba, amma har yanzu tana kasa tana dabo a game da yadda za'a tafiyar da mulkin jihar zuwa gaba. Jam'iyar Greens ta masu da'awar kare muhalli ta sami abinda ya kai kashi goma sha biyu da digo ukku, wanda koda ta hada kai da jam'iyar SPD ba zata sami cikakken rinjaye a majalisar ba. Duk da haka, shugaban jam'iyar ta Greens, Sylvia Lohmann tace:
Yamacin na yau babu shakka zai kasance mai tsawo, kuma ba kamary adda wasu suke nunarwa ba, wnanan yamaci ba zai zama na bakinc iki a garemu ba, a daura dfa haka ma, wanan yaymmaci na farin ciki ne a garemu, saboda nasarorin da muka samu.
Shugaban jam'iyar SPD na kasa baki daya, Sigmar Gabriel ya baiyana farin cikin sa ga sakamakon zaben na jihar Northrhine Werstfalia,, inda yace ranar ta Lahadi, kyakkyawar rana ce ga wannan jiha.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Yahouza Sadissou