1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen Anambara na kan janyo cece-kuce

November 23, 2013

Za a sake kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan da aka gudanar a wasu sassan jihar Anambara a Najeriya, kuma dangane da kura-kuran da aka samu, 'yan sanda za su gudanar da bincike.

https://p.dw.com/p/1AN2a
Attahiru Jega, Independent National Electoral Commission Chairman, declares Nigeria's incumbent President Goodluck Jonathan as the winner of last Saturday's presidential election, in Abuja, Nigeria, Monday, April 18, 2011. Jonathan clinched the oil-rich country's presidential election Monday, as rioting by opposition protesters in the Muslim north highlighted the religious and ethnic differences still dividing Africa's most populous nation. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Attahiru Jega shugaban hukumar zaɓeHoto: AP

Rahotanni daga tarayyar Najeriya na nuni da cewa hukumar zaɓen ƙasar ta sanya ranar Asabar 30 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki domin sake kaɗa ƙuri'a a wasu sasssan jihar Anambra bayan zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 16 ga wannan watan.

Hukumar zaɓen dai ta soke zaɓukan da aka gudanar a wasu sassan jihar bayan da aka zargi jami'an zaɓen da aikata maguɗi, inda daga bisani aka miƙa wa hukumar 'yan sanda domin ta gudanar da bincike kan batun.

Hukumar zaɓen kasar dai ta amince akwai kura kurai wanda hakan ya tilasta soke zaɓen da ake wa kallon na gwaji watanni 18 kafin gudanar da babban zaɓe na ƙasa na shekara ta 2015.

Kakain hukumar zaɓen mai zaman kanta ta Najeriya Frank Egbo, ya ce an sanya sabuwar rana domin a sake gudanar da zaɓen bayan gudanar da ƙwaƙƙwaran binciken dake tabbatar da cewa an aikata kura-kurai a yayin zaɓen da aka gudanar a ranar 16 ga watan na Nuwamba da muke ciki.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinaɗo Abdu Waba