1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin shawo kan rikicin kuɗi a Turai

June 22, 2012

Shugabannin man'yan kasashen Turai huɗu na gudanar da taron share fage a birnin Rome na kasar Italiya bisa rikicin kuɗi da ke addabar nahiyarsu.

https://p.dw.com/p/15Jkh
Italy's Prime Minister Mario Monti, Germany's Chancellor Angela Merkel and France's President Francois Hollande attend an informal EU leaders summit in Brussels May 23, 2012. European leaders will try to breathe life into their stricken economies at a summit over dinner on Wednesday, but disagreement over the issue of mutual euro-zone bonds and whether they can alleviate two years of debt turmoil will dominate the gathering. REUTERS/Francois Lenoir (BELGIUM - Tags: POLITICS BUSINESS) - eingestellt von fab
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban ƙasar Faransa Francois Hollande, tare da wasu shugabannin Turai

Shugabannin gwamnatoci da kuma kasashe hudu da suka fi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai na gudanar da wani taron koli a wannan a wannan juma'a a birnin Rome, domin ci gaba da lalubo hanyoyin magance rikicin kudi da ke addabar nahiyar. Firayim minista Italiya Mario Monti mai masaukin baki ya gayyaci takwaran aikinsa na spain Mariano Rajoy da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma shugaban kasar Faransa Francois Hollande, domin su tsayar da shawara game da mahimman batutuwan da taron koli na Eu zai mayar da hanakali a kai a karshen mako mai zuwa.

Cikin wata hira da ya yi da jaridar "Süddeutsche Zeitung" da ake bugawa a ƙasar Jamus, Monti na Italiya ya nuna bukatar hada karfi da karfe tsakanin manyan kasashen domin ganin bayan matsalar kudi da ta addabi Turai. Firimiya Monti ya kuma kara da cewa samar da tsarin banki na bai daya tsakanin kasashe da ke amfani da Euro zai taimaka wajen kawo karshen matsin tattalin arzikin da ke addabar wasu daga cikinsu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman Shehu Usman