Yunwa ta ragu a duniya in ji FAO | Labarai | DW | 16.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunwa ta ragu a duniya in ji FAO

Wani sabon rahoto da Hukumar Samar da Abinci ta Duniya FAO ta fitar ya nuna cewa yunwa ta ragu amma kuma akwai aiki a gaba idan ana so a cimma muradu karni.

A yakin da ake yi da karancin abinci a duniya, bincike ya nuna cewa a 'yan shekarun baya-bayan nan an sami cigaban gaske. Wannan ya bayyana ne a sabon rahoton da Hukumar samar da Abinci ta duniya wato FAO ta gabatar, inda ta nuna cewa adadin wadanda suka rika fama da yunwa a duk fadin duniya, ya ragu da fiye da milliyan 100. Ko da shi ke a cewar rahoton, bacin wannan cigaban da aka samu, har yanzu akwai akalla mutane milliyan 805 da ke fama da bala'in na yunwa bugu da kari mutun daya a cikin kowane mutane tara na fama da matsananciyar yunwa. Hukumar samar da abincin dai ta ce bisa la'akari da wannan adadi, har yanzu akwai sauran aiki a gaba idan har ana so a cimma muradun karnin da ake kokarain cimma nan da shekara ta 2015, musamman wanda ke yunkurin rage adadin masu fama da yunwa zuwa rabi. Dan haka ne ta yi kira da a inganta matakan da ake dauka cikin gaggawa.

An sami wannan nasara ne a cewar hukumar ta FAO daga yankunan da suka hada da gabas maso kudancin Asiya, da Kudancin Amirka da yankin Karibik. Sai dai a yankin yammacin Asiya da Kudu da saharar Afirka, adadin wadanda ke fama da yunwan ya ma karu ne tsakanin shekaru 20 da suka gabata