Yunkurin yakar cin hanci a kasar Benin | Siyasa | DW | 18.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunkurin yakar cin hanci a kasar Benin

Mahukuntan kasar Benin sun dau salo na ba sani ba sabo kan yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa. Tuni ma wannan shiri ya fara ritsawa da wasu 'yan siyasa na kasar.

Wannan sabon shirin da aka bijiro da shi dai ya fara yin aikinsa na hukunta masu cin hanci da rashawa a kasar Benin inda tuni ya shafi Barthelemy Kassa mamba a jam'iyyar da ke milkin kasar kana tsohon ministan ruwa da makamashi wanda hukumomin shari'ar kasar ke zargi da yin rub da ciki a kan wasu kudade sama da miliyon dubu uku da dari biyar na CFA da kasar Holland ta bai wa kasar domin samar da tsabtataccen ruwan sha ga talakawa.

Symbolbild - Slum in Afrika

Cin hanci na jawo tsaiko wajen yin aiyyukan raya a Benin.

Ga alama dai wannan shiri ya yi wa wasu shugabannin kungiyoyin farar hula na kasar dadi don har ma sun fara yin kiraye-kirayen da majalisar dokokin kasar ta dau mataki na cire masa rigar kariya don ya fuskanci hukunci. Martin Assogba na daga cikin wakilan kungiyoyin farar hular kasar, inda ya ke cewar ''muna ga ya na da muhimmanci a fidda ma shi rigar kariyar domin ya bayyana gaban kotu dan bayar da bahasi akan zargin da ake yi masa''.

Sai dai wasu 'yan kasar ta Benin na ganin akwai tarin mutane na boye a cikin ma'aikatun gwamnati dama na masu zaman kansu wadanda da hadin bakinsu ne aka karkatar da akalar wadannan kudaden. Francis Laleye wani masanin siyasar kasar ta Benin na daga cikin masu irin wannan ra'ayi kuma ya ce ''da wuya mutun daya ya iya aikata wannan barna. Dan haka a ganina ba mutun daya ba ne, mutane da dama ne ke da hannu cikin wannan cuwa-cuwa".

Nigeria Tschadsee Konferenz

Shugaba Boni Yayi da takwarorinsa na Afirka sun dukufa wajen yakar cin hanci.

Yanzu dai 'yan kasar dama duniya sun zura wa 'yan majalisar dokokin kasar ta Benin ido don ganin ko za ta biya bukatar hukumomin shari'a dama sauran 'yan kasar ko kuma za su nemi su kare abokin siyasar ta su ta hanyar kin cire masa rigar kariyar tasa. Babu dai duk wani mataki da hukumomin shari'ar kasar ta Benin za su iya dauka matsawar dai 'yan majalisar dokokin ba su amince su fidda rigar kariya ga abokin tafiyar siyasar tasu ba.

Sauti da bidiyo akan labarin