Yunkurin warware rikicin siyasar Masar | Labarai | DW | 06.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin warware rikicin siyasar Masar

Ana ci gaba da yunkurin diplomasiya domin kawo karshen rikicin siyasar kasar Masar.

Ana ci gaba da yunkurin diplomasiya domin kawo karshen rikicin siyasar kasar Masar, bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Mohamed Mursi. Kawo yanzu kungiyar 'Yan Uwa Musulmai ta ki amincewa da rungumar kaddara kan cewa Mursi ya yi ban-kwana da madafun iko ke nan.

Jakadan musamman nan Kungiyar Tarayyar Turai, Bernardino Leon da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amirka, William Burns, duk sun tsawaita zamansu a kasar, inda suka gana da magoya bayan Mursi da kuma jami'an sabuwar gwamnatin da ke samun goyon bayan sojoji.

'Yan Majalisun dattawan Amirka John McCain da Lindsey Graham na cikin wadanda ke ganawa da sabbin mahukuntan Masar da magoya bayan hambararren shugaba Mursi, domin kwantar da wutar rikicin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi