Yunkurin tsagaita wuta a Libiya | Labarai | DW | 09.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin tsagaita wuta a Libiya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bangarorin da ke fada da juna a Libiya da su tsagaita wuta don bai wa jama'a damar samun sukunin gudanar da bukukuwan Sallah ba tare da fitina ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana mai fatan samun cimma wata kwarya-kwaryar yarjejeniya daga bangarorin biyu da ke yaki da makamai a yau din nan, tare da fatan soma aiki da yarjejeniya tun daga gobe Asabar har  zuwa karshen bukukuwan na babbar sallah.Tun a cikin watan Aprilun wannan shekarar ne sojojin da ke biyayya ga madugun yaki Khalifa Haftar suka yunkuri aniyar kwace iko da birnin Tripoli a hannun gwamnatin hadin kan kasar mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, rikicin.