Yunkurin samun daidaito a rikcikin Siriya | Labarai | DW | 15.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin samun daidaito a rikcikin Siriya

'Yan adawan kasar Siriya da ke halartar tattaunawar neman zaman lafiya kan rikicin kasar a birnin Geneva, sun ce za su shiga gwamnatin rikon kwarya amma da sharadi.

'Yan adawan ta bakin mai magana da yawunsu Salem Al-Meslet, sun ce a shirye suke su shiga cikin gwamnatin rikon kwarya wadda za ta kunshi jami'an diplomasiyya da sauran kwararru na gwamnati mai ci yanzu. Sai dai kuma sun ce ba zasu aminta da kasancewar wadanda aka yi ammanar sun taka rawa wajen halaka jama'a a kasar ta Siriya ba.

A cikin wani kudirinta mai lamba 2254, Majalisar Dinkin Duniya ta yi tsarin kafa gwamnatin rikon kwarya da kuma rubuta wani sabon kundin tsarin mulkin kasar ta Siriya kafin shirya zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa ta 2017. A halin yanzu dai batun makomar shugaban kasar ta Siriya ne dai ke a matsayin abin da ke kawo cikas ga tattaunawar da ake tsakanin bangarorin kasar.