Yunkurin nemar wa yankin arewacin Najeriya ci gaba | Siyasa | DW | 09.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunkurin nemar wa yankin arewacin Najeriya ci gaba

Kwararru daga cibiyar bincike da tarihi ta arewacin tarayyar Najeriya ta gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin halin kace-nace game da makomar yankin da ke zaman kurar baya idan aka kwatanta da kudancin kasar.

Kusan kaso 90 cikin dari na yara da basu zuwa makaranta a cikin tarrayar Najeriya na zaman 'yan asalin arewacin kasar. Ko bayan komawarsa hedikwatar tada hankali da zub da jini sakamakon rigingimu na kabilanci da sabobbin ayyukan barayin shanu, yankin har ila yau ya yi kaurin suna a fannin talauci da zaman kashe wando.

Wadannan muhimman matsalolin ne suka dauki hankalin 'yan bokon yankin da suka gana da shugaban kasar a Abuja a bisa neman hanyar fitar da A'I cikin rama. Sai dai bayan share tsawon lokaci suna ganawa, kwararrun sun ce lokacin neman na kurewa

Muhawara ta yi nisa cikin kasar ta Najeriya bisa rawar Arewa wajen dakile harkoki na kasar. An dai ruwaito gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufa'i na cewar, ruhin Arewa har yanzu yana barci kuma yana tarnaki bisa kokarin ci gaba kasar. Abinda daga dukkan alamu ke nuna irin nisan matsalolin yankin da ke da mafi yawan al'umma, amma kuma koma baya ta kusan nakasa kowanne fanni.

A cikin watan Juni na 2019 ne shugaban kasa Buhari ya nemi daukacin gwamnonin kasar da su tabbatar da tilasta batun ilimi ga daukacin 'yan kasar a matakin farko da ma karamar sekandare a kan hanyar rage jahilci da ma talaucin da ake ta'allakawa da zama bayan.

Sauti da bidiyo akan labarin