1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin maido da tattaunawar Isra'il da Falasdinawa ya ci tura

Usman ShehuJune 30, 2013

Yunkurin sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry na shawo kan bangaren Netanyahu da Mahmud Abbas ya bi ruwa

https://p.dw.com/p/18yiS
U.S. Secretary of State John Kerry, left, meets with Palestinian President Mahmoud Abbas in the West Bank city of Ramallah, Thursday, May 23, 2013. (AP Photo/Jim Young, Pool) pixel
John Kerry da Mahmud AbbasHoto: picture alliance/AP Photo

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya tsawaita ziyarar aiki da ya ke yi a yankin Gabas ta Tsakiya da zummar samun damar sake ganawa da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da kuma firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. Wannan dai shi ne karo na uku da Kerry ke ganawa da shugabannin biyu da nufin neman su koma kan teburin sulhunta rikicin da ke tsakaninsu. Tun gabanin ganawar ne dai ministan tsaron Isra'ila Gilard Erdan ya nuna shakku game da batun sake komawa kan teburin sulhu tsakanin Falasdinu da kuma Isra'ila. Inda kuma daga karshe aka kare tattaunawa farko ba tare da tsinana wani abu ba.

Mawallafi: Mouhamad Awal Balarabe

Edita: Usman Shehu Usman