Yunkurin magance cin hanci a Najeriya | Siyasa | DW | 10.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunkurin magance cin hanci a Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kaddamar da wata majalisa da za ta ba shi shawara kan magance cin hanci da rashawa a kasar.

Majalisar ta mutane bakwai dai ta kunshi manyan kwararru a sassa daban-daban kama daga halayar bil'adama, ya zuwa yin doka da ma tattalin arziki daga manyan jami'oi da cibiyoyi na kasar.

USA Muhammadu Buhari und Barack Obama in Washington

Amirka da sauran kasashen duniya na aiki da Najeriya wajen gano kudaden kasar da aka sace.

'Yan majalisar dai sun hada da Farfesa Femi Adekunle daga jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya, da Farfesa Itse Sagay da ke zaman masanin shari'a da kare hakin bil Adama, sannan kuma da Dr. Benedicta Daudu masaniyar shari'a ta kasa da kasa da ke aiki a jami'ar Jos, sai kuma Farfesa Sadiq Radda kwararre kan hallar bil Adama. Sauran 'yan majalisar dai sun hada da Hadiza Bala Usman da Farfesa Bolaji Owasanye da kuma Farfesa Emmanuel Alemika.

Aikin kwararrun dai ya hada da bayar da shawari kama daga halayar da ta sanya kwasar dubban miliyoyi daga baitulmalin Najeriya dama yanda kasar ta ke iya karbo su idan ta kama daga bankunan da ke Turai da sauran sassa na duniya.

Nigeria Korruption

Kungiyoyin da ke yaki da cin hanci a Najeriya sun yi na'am da matakin shugaba Buhari na yakar cin hanci.

Masana da masharhanta da dama da ke sanya idanu kan yaki da cin hanci na ganin wannan yunkuri zai taimaka wajen sanya shugaban kan hanya a yunkurin da ya ke ya toshe dukannin wata kafa da ke taimakawa wajen bazuwar cin hanci da rashawa kasar.

Dama dai shugaban ya sha nanatawa a irin alkawuran da ya yi lokacin yakin neman zabe cewar zai yi aiki tukuru wajen magance cin hanci da rashawa wanda suka dabaibaiye kasar wajen kaiwa ga irin cigaban da takwarorinta suka samu, baya ga zuar da kimarta a idanun duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin