Yunkurin keta dokar ambaliya a Nuzilan | Labarai | DW | 23.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin keta dokar ambaliya a Nuzilan

Mazauna yankunan da suka fuskanci ambaliya a kasar Nuzilan na yankurin komawa wuraren da suka tsere masu cikin kwanakin nan, duk kuwa da ci gaban da matakan kiyaye jama'a da mahukuntan kasar suka kafa.

Bayanan da ke fitowa daga kasar Nuzilan, na cewa mazauna wasu manyan biranen kasar da suka fusknaci bala'in ambaliya a 'yan kwanakin nan, na kokarin komawa gida, duk da kasancewar dokar ta-baci da gwamnati ta kafa. Daruruwan gidaje ne dai ambaliyar ta lalata a cikin makon jiya, sakamakon batsewar da wani kogi ya yi.

Sai dai bayanan na cewa akwai alamun janyewar ruwa, wanda kuwa shi ne sanadin yunkurin na komawa gida da mazaunan ke yi. Lamarin dai ya yi muni ne a biranen Christchurch da kuma Dunedin.