Yunkurin juyin mulkin da ya ci tura a Habasha ya dauki hankalin Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 28.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Yunkurin juyin mulkin da ya ci tura a Habasha ya dauki hankalin Jaridun Jamus

Yawancin jaridun Jamus sun yi sharhi a kan yunkurin juyin mulkin da aka yi a Habasha da batun tsofin 'yan tawayen Sudan wadanda ke da karfi fada a yanzu da kuma tsarin kasuwanci marasa shinge tsakanin kasashen Afirka.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta sharhinta mai taken "Tuni dubbai suka hallaka." Tsofin mayakan sa kai na Djandjawid a kasar Sudan ke aikata ta'addanci a yankin Darfur, a yanzu sun zama masu fada aji a Khartum babban birnin kasar. 

Jaridar ta ce hotunan da ke fitowa daga Khartum babban birnin kasar Sudan da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani sun tabbatar da cin zarafin da ke faruwa, kama daga azabtarawa da duka da kashe mayakan sa kai. An ciro gawarwaki daga Kogin Nilu. An jibge manyan tankokin yaki da manyan bindigogi. Likitoci sun bayar da rahotannin yi wa mata fyade da kuma harbin kan mai uwa da wabi a kan 'yan adawa. Mayakan na Djandjawid dai sun jima suna cin karensu babu babbaka a yankin Darfur. A yanzu suna kiran kansu da "Rapid Support Forces" suna kuma yin abin da suka dama. An jima ba a jin komai daga yankin Darfur. Tun bayan kifar da gwamantin Omar al Bashir, mayakan sa kan na Djandjawid suke iko da babban birnin kasar. 

Yunkurin juyin mulkin da ya ci tura a Habasha ya yi barazanar mayar da hannu agogo baya

An hallaka shugaban kasar yanki, inji jaridar Süddeutsche Zeitung firaministan Habasha ya bayar da rahoton yunkurin juyin mulki. Jaridar ta ce gwamnatin kasar Habasha ta firaministan Habasha Abiy Ahmed ta bayyana cewa an yi yunkurin yin juyin mulki na yanki a ranar Asabar din da ta gabata. Abiy ya bayyana a gidan talabijin cikin kayan sarki, inda ya bayyana cewar wasu da aka biya kudi sun hallaka shugaban jihar Amhara, Ambachew Mekonnen kana sun hallaka babban hafsan sojojin kasa na kasar, Seare Mekonnen. Gwamnatin dai ta ce al'amura sun koma daidai daga bisani, kana ta sake sanar da mutuwar wasu mutane biyu da suka hadar da tsohon janar na soja da kuma wani babban mai bai wa gwamnati shawara. A cewar gwamnatin wani janar din soja mai suna Janar Asamnew Tsige da ya tsere ne ya shirya juyin mulkin da bai yi nasara ba. An cafke abokan aikinsa masu yawa. Rahotanni sun nunar da cewa a baya-bayan nan Asamnew ya yi kira da a kafa kungiyoyin mayakan sa kai masu dauke da makamai. Tsawon shekaru dai kasar ta Habasha da ke da yawan kabilu, ke fama da rikicin kabilanci, baya ga shafe gwamman shekaru a karkashin mulkin kama karya na 'yan kabilar Tigray da ke zaman tsiraru. Tsawon shekaru 'yan kabilar Oromo da Amharen suka kwashe sun nuna adawarsu da mulkin kabilar Tigray marasa rinjayen, abin da ya kawo karshe da nadin Abiy Ahmed a matsayin Firaminista da ke zaman dan kabilar Oromo da ke da rinjaye a kasar na farko da ya samu wannan mukami. Abiy ya yi kokarin yin sulhu da makwabciyar kasa Eritrea kana ya bayyana aniyar gudanar da sahihin zabe a shekara ta 2020 tare da sakin dubban firsinoni, cikinsu har da jagoran yunkurin juyin mulkin Janar Asamnew Tsige da aka yanke wa hukuncin daurin shekaru tara a gidan kaso. Bayan sakinsa an ba shi mukamin babban jami'in tsaro na yankin Amhara da ke yawan fama da tashe-tashen hankula.

Afirka na kokarin shinfida hanyoyin kasuwanci marasa shinge domin karfafa huldar tattalin arziki tsakanin kasashen

Bari mu sake komawa ga jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung mu karkare da sharhin da ta rubuta mai taken: "Kasuwanci mara shinge a Afirka, wani sabon babi?" Fatan na da yawa, Sai dai kalubalen shi ne aiwatarwa. Kasashen Afirka masu yawa na dakile yin kasuwanci da makwabtansu. Domin cimma buri. Jaridar ta ce a yayin taron kungiyar Tarayyar Afirka AU da za a gudanar a ranar bakwai ga watan Yuli mai zuwa a birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar, za a kaddamar da tsarin kasuwanci mara shinge a tsakanin kasashen nahiyar Afirka African Continental Free Trade Area CFTA a takaice. Kasashe 52 cikin 55 na kungiyar ta AU sun sanya hannu kan yarjejeniyar, Afirka ta Kudu ta ja kafa kafin daga bisani ta rattaba hannu. Sai dai Najeriya da ke da karfin tattalin arziki a Afirkan da Benin da kuma  Eritrea, ba su sanya hannu ba. Sannu a hankali dai tsarin na CFTA zai rage yawan kudin shige da fice a tsakanin kasashen, da kuma samar da kyakkyawar huldar kasuwanci a tsakaninsu da kuma sulhunta rikice-rikice. Daga shekara ta 2020 kuma za a fara tsarin hada-hadar kudi da hakkin mallaka da kuma zuba jari. 

Sauti da bidiyo akan labarin