Yunkurin hana Rasha zuwa gasar birnin Rio de Janeiro | Labarai | DW | 21.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin hana Rasha zuwa gasar birnin Rio de Janeiro

An dai samu 'yan wasan na Rasha da dama a badakalar shan kwayoyi da ke kara kuzari 'yan wasa.

Symbolbild Leichtathletik Russland Doping

Badakalar amfani da kwayoyi sanannan abu ne tsakanin 'yan wasa

Kotun kasa da kasa da ta saurari korafe-korafen wasanni a ranar Alhamis din nan ta yi watsi da daukaka karar 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Rasha wadanda ke neman kotu ta dauki mataki da zai hana haramta musu zuwa gasar wasanni a Brazil, abin da ke nuna akwai yiwuwar kwamitin da ke shirya wasannin na Olympic zai iya dakatar da Rasha daga halartar wasannin kasa da kasa na Olympic da za a yi a birnin Rio de Janeiro na Brazil, saboda zargin badakalar da ta shafi amfani da kwayoyi da ke sa kuzari a tsakanin 'yan wasa a lokutan wasanninsu na baya.

A ranar Lahadi kwamitin na IOC zai zauna inda a nan ne zai bayyana ko za a dakatar da kasar ta Rasha daga halartar wasannin na Rio de Janeiro a Brazil da za a fara daga ranar biyar ga watan Agusta mai zuwa ko kuma a'a.