Yunkurin dawo da huladar Amirka da Cuba | Labarai | DW | 10.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin dawo da huladar Amirka da Cuba

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya gana da takwaransa na kasar Cuba Bruno Rodriguez a taron kolin kasashen Latin Amirka da ke gudana Panama.

Wannan shi ne ganawar manyan jami'an gwamnatin kasashen biyu tun shekarun 1950. Ba a dai fayyace mi aka tattauna ba a ganawar ta su. Shi ma shugaban kasar ta Amirka Barack Obama ya isa Panama, inda ake saran zai gana da shugaban kasar Cuba Raoul Castro, ganawarsu ta farko a hukumance cikin kokarin da kasashen biyu ke yi na farfado da huldarsu. A watan Disamban bara ne kasashen biyu, suka amince da maida hulda tsakaninsu. Wannnan dai shi ne karon farko da kasar Cuba ke halartan taron kasashen Latin Amirka. Tun a jiya ne dai, ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta fidda sanawar da ke bukatar fidda kasar Cuba cikin jerin kasashen da ke goyon bayan ta'addanci.