Yunkurin dakile shiga Turai daga Najeriya | Zamantakewa | DW | 12.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yunkurin dakile shiga Turai daga Najeriya

Wata kungiya ta tarayyar Najeriya ta hada gwiwa da hukumar shige da fice ta kasa wajen wayar da kan jama’a kan hatsarin da ke tattare da bi ta haramtacciyar hanyar hamadar Sahara don zuwa nahiyar Turai.

Ana ci gaba da samun karuwar ‘yan Najeriya da ke kaura daga kasarsu zuwa Jamhuriyar Nijar da Libiya da nufin tsallakawa nahiyar Turai  duk da hatsarin da yake tattare da shi, inda da dama daga cikinsu ke rasa ransu a hamadar sahara. Wannan ne ya sanya kungiyoyi masu zaman kansu suka kara kaimi na wayar da kan jama'a kan hatsarin da ke tattare da lamarin.

Hangen aljannar duniyar da masu yin kaura ta haramtacciyar hanya ke yi ya sanya Kungiyar da ke nemo dabarun dakile wannan matsala a Afirka  tinkarar aiki na wayar da kan jama'a musamman matasa maza da mata a Najeriyar.

Kokari na aiki tare da zummar samun nasara ya sanya kungiyar aiki tare da hukumar kula da shige da ficen jama'a ta Najeriya saboda ita ce a hukumance aka dora wa nauyin dakile masu wannan mummunan dabi'a. Alhaji Muhammad Baban Dede shi ne shugaban hukumar ya bayyana matakan da suke dauka na aiki tare da irin wadannan kungiyoyi.

Hada karfi a tsakanin kasashen duniya da ma kungiyoyi irin wannan zai yi tasiri wajen dakile kwararar baki da ke kaura ta haramtacciyar hanya mai hatsarin gaske daga Afirka zuwa nahiyar Turai ta hamadar Sahara da zai taimaka ceto rayyukan milliyoyin mutane da ke shiga hatsari.

 

Sauti da bidiyo akan labarin