YUNKURIN DAIDAITA ALBASHIN ÝAN MAJALISAR TURAI YA CI TURA. | Siyasa | DW | 27.01.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

YUNKURIN DAIDAITA ALBASHIN ÝAN MAJALISAR TURAI YA CI TURA.

Sabon yunkurin da `yan majalisar tarayyar Turai suka yi na daidaita albashinsu, don rage bambancin da ake da shi tsakanin albashin wadanda suka fito daga kasashe mawadata da matalauta na nahiyar, ya ci tura. Za a dai ci gaba ne da tsarin da ake da shi kawo yanzu, inda a lal misali wasu `yan majalisar daga Italiya suke samun albashin Euro dubu 11 a wata, yayin da takwarorinsu na kasar Poland ke samun Euro dari 6 kawai. Duk masu biyan haraji a kasashen kungiyar dai suna ta kara bayyana mamakinsu ga yadda, ake ta kashe kudi ba gaira ba dalili a kan `yan majalisar. Ban da dai albashinsu, wasu `yan majalisar na samun alawas na tafiye-tafiye da dai sauransu na Euro dubu 8 a wata.

Wannan batun na kayyade albashin `yan majalisar dai, an dade ana ta korafi a kansa. Ko yaushe aka takalo batun kuwa, sai ka ga jaridu da wasu mujallu sun yi ta kururuwa kan cewa, masu tsara dokokin suna cin karensu ne babu babbaka. Wannan salon dai, shi ke tunzura jama'a su yi ta kai kararraki gaban kotuna ko kuma gwamnati. Ita ko gwamnatin, don kare kanta, sai ta dau wasu matakai, wadanda idan aka yi nazarinsu sosai, sai a ga cewa, babu wani dalilin daukansu. Ta hakan ne dai, shugaba Schröder na nan Jamus, ya hau kujerar na ki a taron Hukumar Tarayyar Turan, game da batun daidaita da kuma kara wa `yan majalisar Turan albashi. Ya yi hakan ne kuwa, kawai saboda wasu makalan da ba su da tushe da jaridar nan ta BILD-Zeitung ta yi ta bugawa a jere.

Daidaita albashin `yan majalisar, zai iya janyo kau da magudin da ke wakana a halin yanzu a kungiyar EU. Akwai `yan majalisa da yawa, wadanda suka fi gwammace wa tsohon tsarin da ake aiki da shi, saboda ta hakan ne suke iya tabka magudi daban-daban, inda kuma a ko wane wata suke ta kwasan kudaden haraji da al'umma ke biya. Babu shakka, shhirin da `yan majalisar Turan suka gabatar na daidaita albashinsu da kuma yi musu kari, yana bukatar gyara. Amma wannan ba dalili ba ne na sa kafa a shure shi gaba daya.

Matakin da aka dauka yanzu dai, ya janyo hauhawar tsamari tsakanin shugaban Majalisar Turan Pat Cox, da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder. Amma saboda zaben `yan majalisar da za a yi a cikin watan Yuni mai zuwa, Pat Cox ya fi gwammacewa ne ya tinkari wannan lamarin ta hannunka mai sanda. Tambayar da mafi yawan al'umman Turan ke yi dai ita ce, wai me ya sa ne kungiyar EU ke ta kashe makudan kudade kan majalisar, wadda ke da cibiyoyi a birnin Brussels da kuma Strabbourg k A wannan zamani da ake ta daukan matakan tsimi da kara haraji, ai bai kamata a ce kungiyar sai kara kashe kudi take yi ba. A zahiri dai, jama'a da yawa na ganin cewa kudin Euro miliyan dari da ake kashewa ko wace shekara a kan Majalisar Turan bai cancanta ba. Fadada kungiyar da za a yi ma, zai kuma kara habaka jumlar kudin da za a yi ta kashewa kan majalisun na gaba. Amma a halin yanzu, wadannan majalisun ba su da wani cikakken iko na zartaswa. Duk shirin da suka gabatar, sai gwamnatocin kasashen kungiyar Hadin Kan Turan sun amince da shi kafin ya zamo doka. To in ko haka ababan za su ci gaba da kasancewa, wasu masharhanta na ganin cewa, kafa majalisun Turan da kuma dimbin yawan kudaden harajin da ake ta kashewa a kansu, ba su da wata ma'ana ke nan.
 • Kwanan wata 27.01.2004
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvmI
 • Kwanan wata 27.01.2004
 • Mawallafi Yahaya Ahmed.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvmI