Yunkurin ceto tattalin arzikin Tunisiya | Labarai | DW | 20.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin ceto tattalin arzikin Tunisiya

Asusunn IMF ya ce yana tattauna batun baiwa Tunisiya rancen kudi na dubbannin miliyoyin dalar Amirka domin inganta rayuwar al'umma.

NEW YORK, NY - SEPTEMBER 27: Moncef Marzouki, President of Tunisia, addresses the United Nations General Assembly on September 27, 2012 in New York City. The 67th annual event gathers more than 100 heads of state and government for high level meetings on nuclear safety, regional conflicts, health and nutrition and environment issues. (Photo by Mario Tama/Getty Images)

Shugaban Tunisiya, Moncef Marzouki

Wata mai magana da yawun asusun bayar da lamuni a duniya na IMF Wafa Amr, ta bayyana cewar asusun na tattaunawa tare da hukumomin kasar Tunisiya game da baiwa kasar rancen kudin daya wansa ya zarta dala miliyan dubu bakwai. Kakakin asusun ta sanar da hakan ne jim kadan bayan da takaddamar siyasa ta tilastawa firayi ministan kasar Hamadi Jebali yin murabus. Ta ce da zaran hukumomin na Tunisiya sun sanar da kafa sabuwar gwamnati, asusun zai nemi sanin kudirin da ke gabanta, kuma da zaran harkokin siyasa sun daidaita, to, kuwa asusun zai yi nazarin hanyar tallafawa kasar ta Tunisiya.

A halin da ake ciki kuma, ana sa ran nada sabon firayi minista a kasar ta Tunisiya, bayan da tsohon fitayi ministan ya yi murabus, sakamakon gaza samun goyon bayan jam'iyyar sa wajen yunkurin da yayi na kafa gwamnatin kwararru domin tafiyar da lamura a kasar, wadda ke zama cibiyar juyin juya halin daya yi awon gaba da kujerun wasu shugabanni a kasashen Larabawa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal