Yunƙurin sauya shugabancin majalisar dokokin Najeriya | Siyasa | DW | 21.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunƙurin sauya shugabancin majalisar dokokin Najeriya

Jami'yyar adawa dake da rinjaye a Majalisar dokokin ta ce wajibi ne a mutuntu tanadin dokokin da suka girka majalisa a baiwa masu rinjaye jagoranci

Majalisar datawan Najeriya ta bayyana sunayen mutane 12 da shugaban ƙasar Goodluck Jonathan ya gabatar mata don ta amince a nadasu minister, yayinda wata hatsaniya ta kaure a zauren majalisar wakilan Najeriya bisa yunƙurin yan jami'yyar APC na sauya shugabancin majalisar .

To hayaniyar dai ta ɓarke ne a lokacin zaman majalisar wakilan Najeriyar wanda 'ya'yan jami'yyar adawa ta APC da suke cike da kudurin ganin sun aiwatar da sauyi a shugabacinta, suka nuna basu haƙura ba duk da katse masu hanzarin ƙudurin na su da wata kotu ta yi, domin kuwa kalaman da shugaban masu rinjaye Femi Gbajabiamila ya yi ya harzuka wasu yan majalisar.

Abinda yafi ɗaukan hanakali shi ne yadda jami'yyun biyu na PDP da APC suka rasa wakilansu biyu kowanensu a majalisar, abinda Hon Alhassan Ado ya bayyana cewa alama ce mai kyau ga yadda ala'ammura ke gudana.

Maƙasudin wannan yunƙuri

"Har yanzu lissafin da muke da shi da alkalumanmu bai canza ba, biyu sun karu biyu sun fita har yanzu jamiyyar APC ita ce ke da rinjaye a majalisar waklilai ta tarayyar Najeriya. Abinda ya faru abin sha'awa ne domin kuwa jamiyyar PDP da ke iƙirarin duk wanda ya canza sheƙa za ta sa a kori kujerarsa to yau ga ‘yayan wata jamiyyar sun koma PDP sai muga abinda alakalan Najeriya zasu yi. Amma batun sauya shugabanci a majalisar nan musamman maganar rinjaye da rashin rinjaye wannan na nan daram ba zamu sauya ba, abinda muka yi shine mun dan dakata ne kawai saboda ga umurnin kotu''.

Sunayen waɗanda shugaban ƙasa ke son naɗawa minista

Majalalisar datawan Najeriya kuwa ta bayyana sunayen mutane 12 da shugaban Najeriya ya aike da su domin neman amincewa a naɗasu bisa mukamin ministoci. Sunayen da suka kasance cike da bazata domin kuwa sun hada da Janar Aliyu Gusau daga jihar Zamfara da Ambassador Aminu Wali daga jihar Kano da kuma Mr Boni Haruna tsohon gwamman jihar Adamawa. Har ma da Musliu Obanikoro daga Lagos Sanata Ahmad Lawal ya bayyana mataki na gaba da zasu dauka a kan sunayen da aka turo.

‘'Majalisa za ta yi aikinta bisa abinda ya kamata ta yi, domin sai yanzu ne ya kawo sunan amma kuma ya dade cire wasu ministocin kuma sai yanzu ya kawo sunayen amma haka ya yi ta aikinsa. Saboda haka majalisa zata zauna ne ta duba a huruminta a kan tattance wadanda ake son su zama ministoci. Saboda ba dai dai bane shugaban kasa ya ki yin aikinsa a kan lokaci, amma da an kawo sai ace majalisa ta rike, A'a majalisa zata yi akinta yadda ya kamata

Me wannan mataki na shugaban ke nufi?

A karon farko shugaban Najeriyar ya aikawa majalisar da sunayen manyan hafsoshin kasar da ya zaba domin ta tantance su, to ko me wannan ke nunawa? Har ila yau ga Sanata Ahmed Lawal bayyana cewa.

A yayinda har yanzu majalisar wakilan Najeriyar kle ci gaba da yunkurin lallai sai ta sauya shugabancin majalisar bisa ga rinjayen da jamiyyar APC ked a shi a yanzu, a majalisar datawa kuwa bayanai sun nuna cewa ya zuwa yanzu akwai sanataoci 16 da suka rattaba hannunsu don amincewa su sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Da alamun da sauran yan kalo a kan canza sheka da sauyin da za'a gani a shugabancin majalisar a nan gaba, a dai dai lokacin da guguwar siyasar da ke kadawa a Najeriyar ke kara turnikewa musamman saboda fuskantar zabe.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Pinaɗo Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin