Yunƙurin samar da zaman lafiya a Kwango | Labarai | DW | 26.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunƙurin samar da zaman lafiya a Kwango

Jami'ar kula da harkokin ƙetare ta Ƙungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton, ta yi kira ga 'yan tawayen Kwango da masu ruwa da tsaki a yankin domin samar da zaman lafiya a Kwango.

©Kyodo/MAXPPP - 11/12/2012 ; GOMA, Democratic Republic of Congo - Soldiers of the M23 rebel movement hold weapons aboard a vehicle in Sake near Goma, the Democratic Republic of the Congo, on Nov. 30, 2012. (Photo by Takeshi Kuno) (Kyodo)

'Yan tawayen ƙungiyar M23

Kiran nata ya biyo bayan ƙazamin faɗan da ya ɓarke ne, kwanaki ƙalilan bayan rushewar tattaunawar sulhu tsakanin ɓangarorin. Sanarwa daga ofishin Ashton da ke birnin Brussels, na bayyana damuwa dangane da faɗan da ya shiga rana ta biyu ana gwabzawa a yankin arewa maso gabashin ƙasar ta Kwango.

A kan haka ne ta yi kira ga ƙungiyar 'yan tawaye ta M23, da ta darajata yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a taron da ya rushe a ranar Litinin a birnin Kampala na Yuganda. Hukumomin Ruwanda da ke makwabtaka, sun zargi sojojin Kwango da harba makamai zuwa cikin ƙasar, tare da yin barazanar mayar da martani idan aka ci gaba da harbin.

Mawallafi : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdourahamane Hassane