Yunƙurin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa | Siyasa | DW | 29.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunƙurin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa

Kotun tsarin mulkin Nijar ta ce shugaban ƙasa na da hurumin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa, lamarin da ya janyo mahawara a tsakanin al'umma.

epa02847783 President Mahamadou Issoufou of Niger during a meeting with US President Barack Obama and fellow African leaders from Niger, Benin, and Guinea, in the Cabinet Room of the White House, in Washington DC, USA, 29 July 2011. EPA/MARTIN H. SIMON / POOL +++(c) dpa - Bildfunk+++

Mahamadou Issoufou

A cikin wata wasiƙa da shugaban gomnatin Nijar Briji Rafini ya rubuta kana ya aike wa kotun tsarin milkin a ranar 23 ga wanann wata na Yuli ya buƙaci da ta fitar da jaki daga duma a game da hallarci ko kuma haramacin wanann ɓuri na shugaban ƙasa na kafa gwamnatin haɗin kan 'yan ƙasa da za ta iya bai wa 'yan adawa damar a dama da su a cikin harkokin mulki.

Kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa bai saɓama doka ba


Presidential candidate Seini Oumarou, a former prime minister under deposed president Mamadou Tandja, casts his vote in Niamey, Niger, Monday, Jan. 31, 2011. This impoverished country on the edge of the Sahara took another stab at democracy Monday when it voted for a new president and parliament that are expected to take over leadership from the military.(Foto:Tagaza Djibo/AP/dapd)

Seyni Oumarou jagoran 'yan adawa

Kotu dai ta ce matakin bai saɓawa kudin tsarin mulkin ba, kuma ta ce ya hallarta inda ƙasar ta shiga cikin wani mawuyacin hali ta kan iya yin haka. To sai dai Maina Karte wani masanin ilimin dokokin tsarin mulki ya ce yana da ja akan wanan ra'ayi na kotun.

''Da farko gwamnatin haɗin kan ƙasa kalmma ce da babu ita a cikin tsarin mulki na ƙasa, yin haka ya saɓama doka.''

'Yan adawa sun ce ba za su shiga cikin sabuwar gwamnatin ba

Archivbild vom 6. Dezember 19965 zeigt den Präsidenten von Niger, Mahamane Ousmane, bei einem Besuch der Elfenbeinküste. Das Militär in dem westafrikanischen Staat hat den Präsidenten am Samstag durch einen Putsch gestürzt. Der entmachtete Ousmane war im April 1993 als erstes Staatsoberhaupt Nigers demokratisch gewählt worden.

Mahamane Ousmane matamaikin jagoran ' yan adawa kana tsohon shugaban ƙasar Nijar

Watanni kimanin bakwai kennan da shugaban ƙasa ke ta faman yin tayin kafa gwamnatin haɗin kan ga 'yan adawa na ARN, amma kuma sun yi watsi da shirin a bisa hujjar cewa hakan ya sabawa dokokin Nijar. To ko yaya 'yan adawar su ka karɓi wanann ra'ayi na kotun. Alhaji Dudu Rahama shi ne kakakin kungiyar 'yan adawa na ARN.

''Za mu shiga gwamnatin idan hukumomin sun cika wasu sharuɗa da ƙungiyar mu ta gabatar musu, waɗanda nan gaba za mu bayyana waɗanan sharuɗa.''

Yan Nijar da dama ne dai ba su amince ko kaɗan ba da wannan shiri na gwamnatin haɗin kan ƙasa wanda suke yi wa kallon wani game kai tsakanin 'yan adawa da kuma gwamnatin domin ci da gumin talakawa. Kuma yanzu haka jama'a sun zura ido suna jiran ganin abin da zai biyo baya akan wannan batu wanda hankali al'umma ya karkata akai.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto da kuma wanda wakilinmu na Tahoua Salissou Boukari ya aiko mana dangane da ra'ayoyin jama'a a kan kafa gwamnatin ta haɗin kan ƙasa.

Edita: Gazali Abdou Tassawa
Edita Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin