yunƙurin inganta masana′antu a Afirka | Siyasa | DW | 20.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

yunƙurin inganta masana'antu a Afirka

20 ga watan Nuwamba ranar ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin yin nazarin ci gaban masana'antu a cikin ƙasashen nahiyar Afirka.

A Najeriya durƙushewar manya da ƙananan masaƙu da kampanoni masu zaman kansu ne suka haifar da koma baya ga ayyukan masana'antun a cikin ƙasar, sakamakon mutuwar su,waɗanda suka janyo shigowar kayayyakin ƙasashen ƙetare a cikin ƙasar

Jama'a da dama sun rasa aiki a Najeriya saboda durƙushewar kampanoni

Ma'aikatan Masuƙu da Kampanoni ne da dama suke kokawa game da durƙushewar ɗarurruwan masaƙun da ƙananan masana'antu da kampanonin da suka mutu saboda rashin kulawa. El-yakub Saidu shi ne Tsohon Shugaban ƙungiyar Ma'aikatan Masaƙun a Garin Kaduna.Ya ce: '' Mu dai a nan Najeriya baƙin cike ne muke yi a rana irin ta yau,saboda mutuwar masaƙu kusan guda 12 waɗanda suka ƙunshi sama da ma'aikata dubu. Da dama daga cikin ma'aikatan sun mutu ba tare da samun kuɗaɗensu ba na fansho. lalacewar masaƙu ya sanya 'yan Najeriya ba sa ɗaukarsu da daraja.Duk wani kaya da aka ƙerashi a cikin ƙasar ba ya samun karɓuwa daga jama'a.Rahotanni sun nunar da cewa akwai Kampanonin Najeriya da yawan gaske da suka yi hijira zuwa wasu ƙasashen Afirka inda ba sa fuskantar matsalar ƙarancin wutar lantarki, kamar yadda suke fama da shi a cikin Najeriya.

Nazari na ƙwararru a kan ci gaban masana'antu a Afirka

Bugu da ƙari ƙwararrun masana kan tattalin arzikin ƙasa sun ci-gaba da nunar cewar mutuwar masana'antun yanzu haka dai sun haifar da babban komabaya a ɓangaren ɓunkasa tattalin arzikin ƙasa da suka kawo kan ƙaruwar masu zaman kashe wando.Alhaji Mohammed Auwal Maƙarfi ya kasance wani babban jigo ne a cibiyar ɓunkasa masana'antu da tattalin arziki a Najeriya da shi ma ke nuna ɓacin ransa bisa ga yadda durƙushewar Masuƙo da suka zamo tamkar Matattun kangaye,

Ya ce : ''Gaskiyar magana ita ce yawancin masaƙun sun lalace domin a kwai abubuwa da dama da suka haɗa da rashin samun tallafi wannan shi ne babban dalilin mutuwar masana'antu.''A Jihohin Arewa dai baya ga dubban masuƙu da kampanoni da suka lalace da aka ginasu lokacin mulkin Sardauna,akwai wurarre irin su bankin arewa,da gidan radio Nigeria Kaduna,da kampanin Tattalin arzikin Arewa NNDL,da New Nigerian New Paper waɗanda mutuwar iri-irin waɗannan kampanoni babban koma baya ne ga yanki.Ya zuwa wannan lokaci dai a sakamakon ƙaruwar mutuwar masaƙu da ƙananan masana'antu a Nigeria ,sun haifar da ƙaruwar giggina sabbin masana'antun ƙasar China waɗanda suka mamaye kasuwannin Najeriya.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da wakilinmu na Abuja Ubale Musa ya aiko mana dangane da yajin aikin kampanonin sufirin jiragen sama, da kuma hira da Leetafa Mustafa ta yi da Abdulahi Soli wani masannin tattalin arziki a Niger.

Mawallafi : Ibrahima Yakubu
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin