1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin magance rikicin siyasa a Thailand

May 20, 2014

Firaministan Thailand Niwattumrong Boonsongpaisan ya yi kira da a gudanar da zaɓe a watan Agusta mai zuwa domin kawo ƙarshen rikicin siyasa da ƙasar ke fama da shi.

https://p.dw.com/p/1C37z
Hoto: Kazuhiro Nogi/AFP/Getty Images

A wani yunƙuri na neman warware rikicin siyasar ƙasarsa, firaministan Thailand da ke riƙon kwarya Niwattumrong Boonsongpaisan ya ba da shawara da a gudanar da zaɓen 'yan majalisa na gama da wa'adi a ranar uku ga watan Agusta ta wannan shekarar da muke ciki. Wannan ya zo ne a daidai lokacin da 'yan adawa ke tada kayar bayan tun watannin shidda da suka gabata domin tilasta wa gwamnati yi murabus.

Tuni dai sojojin Thailand suka kafa dokar da ke bai wa soji damar amafni da ƙarfi idan zarafi ya kama domin wanzar da zaman lafiya a kasar. Babban hafsan sojin kasar Prayuth Chan-Ocha ya haramta wa masu zanga-zanga a Bangkok fantsama a kan tituna, tare da haramta sanya duk wani shiri a kafafen watsa labaran ƙasar da ake ganin zai jawo tada zaune tsaye. Chan-Ocha ya kuma ce ƙarƙashin dokar 'yan sanda na da izinin neman agajin sojin ƙasar wajen kwantar da tarzoma idan buƙatar hakan ta taso, sai dai a daura da wannan gwamantin ƙasar ta ce rundunar sojin ƙasar ta yi gaban kanta ne wajen sanya dokar domin ba a tuntuɓeta ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahamane Hassane