1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin gwamnati na daidaita al'amuran tsaro a Najeriya

March 12, 2013

Majalisar mashawartan ƙasar ta tattauna sabon halin rashin tsaro da ƙasar ta sami kan ta a ciki.

https://p.dw.com/p/17vlI
Soldier patrol to monitor protesters at Ojota district in Lagos on January 16, 2012. Nigerian security forces fired tear gas and shot into the air Monday to disperse around 300 protesters in Lagos as authorities moved to prevent demonstrations in various parts of the country. Nigerian unions announced on January 16 they were suspending a week-old nationwide strike over fuel prices which has shut down Africa's most populous nation and brought tens of thousands out in protest. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images/AFP

Sannu a hankali dai karatun na neman wucewa da sannin mahukuntan Tarrayar Najeriyar, da suka zura ido suka kalli kisan baƙi yan ƙasashen waje har kusan guda goma cikin ƙasar a tsawon wattani goma da suka gabata.Hankali dai na tashe a fadar shugaban ƙasar ta Asorock tun bayan kisan wasu baƙin ma'aikatan wani kamfani a ƙarshen mako.Ta kuma girka wata kafa ta taruka da nufin neman hanyar fuskantar sabon ƙalubalen da ke ƙara fitowa fili da gazawar ta hukumomin Najeriyar.

Tarrayar ta Najeriya na buƙatar sami haɗin kan dukkanin al'ummar.

An dai share tsawon wunin jiya ana ganawar tsaro ta sirri a tsakannin manyan hafsoshin tsaron Tarrayar, da shugabnnin majalisar, Kafin wani sabon taron majalisar mashawartan ƙasar. Wacce ta ƙunshi tsofaffin shugabannin ƙasar da gwamnonin 36 da kuma shugabannin ɓangaren shari'a da suma suka share tsawon awoyi suka kuma fito suka shaidawa yan jarida ƙasar cewar Najeriyar na cikin babban hatsarin da ke buƙatar hannun kowa a faɗar Admiral Murtala Nyako mai ritaya da ke zaman gwamnan jihar Adamawa kuma ɗaya daga cikin mahalarta taron.Batun na rashin tsaron dai ya kai ga kusan baiwa hammata iska a shi kansa zauren tsaron a tsakanin gwamnan jihar Edo Adams Oshomhole da kuma ministar shari'ar ƙasar Muhd bello Adoke.Oshomhle da ya daɗe yana zargin hannun jam'iyyar PDP da hannun cikin kisan wani jami'in gwamantinsa, ya kai ga kusan kwasar 'yan kallo da ministan da ya nemi yi masa shaguɓe game da kisan da ya tada hankalin jihar ya kuma ƙara fitowa fili da irin ruɗun da yanzu haka ƙasar ta ke daɗa fuskanta.

NIGERIA topographical map highlighted, with WARRI and LAGOS locators, partial graphic
Hoto: AP Graphics

Ya ce ''An kashe mun babban sakatare na, ba wanda ya damu kuma ina fafutukar tabbatar da gaskiya domin ba da girma ga mutumin da ya sadaukar da rayuwar sa. Amma kuma ga wani da bai damu da rai ba, wanda ya ɗauki rayuwa abin wasa ce ni ba haka nake ba. Babban makasudin gwamanti shi ne ba da kariya ga rai da dukiyar alummar. Ko a cikin tsananin talauci ya kamata mutane su samu yaƙinin suna da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ba wanda ya ke da iko a ƙarkashin kundin tsarin mulkin mu, ya ɗau rai ba tare da bin ƙa'idojin kotu ba.''

Jiran ganin sabon matakin da gwamnati zata ɗauka domin magance matsalar tsaro

A bara ne dai wasu da ba'a san ko su wanene ba suka hallaka Olaitan Oyerinde sannan kuma yan sanda da jami'an bincike na hukumar tsaro suka fitar da mutane daban daban a matsayin makisan jami'in.Abin jira a gani dai na zaman mataki na gaba ga gwamantin da har yanzu ke fuskantar ƙaulbalen gano wasu faransawa har takwas da ake jin suna cikin Najeriya suna kuma hannun sabuwar ƙungiyar da ake ta'allaƙawa da AlQaida a cikinta.

Photograph made available 25 January 2010 shows a Nigerian women walking past soldiers patrolling in the Nigerian city of Jos following a week of religious violence in the central Plateau district, Nigeria 22 January 2010. Fighting between gangs of Christian and Muslim youths claimed more than 300 lives with millions of Naira worth of properties destroyed and hundreds of people displaced. EPA/GEORGE ESIRI
Hoto: picture-alliance/dpa

Daga asa za a iya sauraon wannan rahoto

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Abdourahamane Hassane