1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama Bobi Wine daga wuren taron da gwamnati ta haramta

Ramatu Garba Baba MNA
April 22, 2019

'Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa dandazon magoya bayan mawaki Bobi Wine wanda ya rikide ya koma dan siyasa, kafin daga bisani su yi awon gaba da shi.

https://p.dw.com/p/3HEBp
Uganda - Bobi Wine (Sänger) mit Krücken in Gerichtssaal in Gulu
Hoto: Getty Images/AFP

Amfani da karfin da jami'an tsaron kasar Yuganda suka yi wajen tarwatsa magoya bayan Bobi Wine ya haifar da rudani. Wine wanda yanzu dan majalisa ne ya shirya amfani da taron ne don sanar da manema labarai halin da ake ciki bayan da ya karbi umarnin gwamnati kan soke taron bikin.

Sa-in-sa a tsakaninsa da bangaren gwamnati ya soma ne bayan da aka zarge shi da hannu a jifan tawagar Shugaba Yoweri Museveni lokacin yakin neman zaben cike gurbi na majalisar dokoki.

Mawakin da ya rikide ya koma dan siyasa, ya ce shi dai yana gwagwarmaya da Shugaba Museveni ne domin tabbatar da 'yancin fadin albarkacin baki a kasar ta Yuganda.