Yiwuwar tsagaita wuta a Yemen | Labarai | DW | 10.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yiwuwar tsagaita wuta a Yemen

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci samun tazarar wasu 'yan sa'o'i don bada damar mika agaji ga wadanda ke bukata a Yemen

Majalisar ta nuna wannan bukatar ce yayin da, da ita, da kuma kungiyar agajin nan ta Red Cross suka isa da rukunin farko na kayan agaji cikin kasar ta Yemen a yau Juma'a. Hakan kuwa na zuwa a dai dai lokacin da birnin Aden da ke kudancin kasar ya fama da luguden wuta da mayakan hadin gwiwa suka kaddamar kan 'yan tawaye cikin daren jiya.

A farkon wannan makon ma dai kungiyar likitocin nan da ke taimakawa kasashe ta Doctors Without Boarders, ta isa da wasu kayayyakin na agaji a birnin Aden dake kudancin kasar. Sai dai babban jami'in na MDD Yohannes Klaauw, ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa akwai bukatar karin kayan na agaji, saboda karancin wadanda suka kai a yanzu.

Akalla dai tan 16 na magunguna dama na abinci ne ke cikin kayayyakin da suka sami isa kasar.