Yiwuwar samun rikici a gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 08.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yiwuwar samun rikici a gabas ta tsakiya

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a yankin gabas ta tsakiya ya ce akwai yiwuwar samun tashin hankali sakamakon matsayin da Amirka ta dauka na ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Nikolay Mladenov ya shaidawa kwamitin sulhu na majalisar cewar ya damu kan halin da yankin zai shiga sakamakon wannan matakin na Amirka inda ya ke cewar dole a dauki matakai na ganin lamura ba su rikice ba. Mladenov na wadannan kalamai yayin wani taro da aka kira kan wannan batu wanda kasashen duniya ke cigaba da nuna rashin jin dadinsu kan matakin kasar ta Amirka. Mutane da dama dai sun yi zanga-zanga yau a birnin Kudus inda suka yi ta Allah wadai da batun har ma rahotanni suka ce mutum guda ya rasu bayan da aka samu wata arangama tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga.