1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar kawo karshen rikicin Ukraine

August 18, 2014

Wata tattaunawa da aka yi tsakanin Rasha da Ukraine karkashin jagorancin Jamus da Faransa da ke shiga tsakani ta sanya fatan warware rikicin Ukraine din.

https://p.dw.com/p/1CwCR
Hoto: Reuters

Ministan harkokin kasashen ketare na Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce an samu ci gaba mai ma'ana a tattaunawar da suka yi a birnin Berlin da takwarorinsa na Ukraine da Rasha da kuma Faransa, domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen warware rikicin Ukraine. Steinmeier ya ce akwai yiwuwar su ci gaba da tattaunawa a ranar Litinin ko Talata domin samo hanyar tsagaita wuta a Ukraine a yakin da mahukuntan Kiev ke gwabzawa da 'yan aware masu goyon bayan Rasha a gabashin kasar da kuma iko da kan iyakar kasashen Rasha da Ukraine da ma kai kayan agaji yankin gabashin Ukraine da ke tsananin bukatar taimako. Ita ma dai ma'aikatar harkokin waje ta kasar Rasha ta ce an samu ci gaba a tattaunawar tasu, wanda ta ce tana fatan hakan zai taimaka wajen kawo karshen rikicin Ukraine din. Sai dai a nasa bangaren ministan harkokin kasashen waje na Ukraine Pavlo Klimkin ya ce shi bai ga wani ci gaba da aka samu ba a tattaunawar tasu kasancewar akwai sauran muhimman abubuwa da ya kamata a yiwa duba na tsanaki.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal