Yiwuwar hadewar kungiyoyin ′yan ta′adda waje guda | Siyasa | DW | 10.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yiwuwar hadewar kungiyoyin 'yan ta'adda waje guda

Mubayi'ar da Boko Haram ta yi wa kungiyar IS na nuna alamun yiwuwar samun hadewar kungiyoyin masu kaifin kishin addinin Islama waje guda musamman ma a Afirka.

A kwanakin baya ne kungiyar Boko Haram ta nuna goyon bayanta ga kungiyar nan ta IS da ke fafutuka wajen kafa daular Islama a Siriya da Iraki to sai dai duk da wannan kungiyar na fuskantar kalubale babba a yunkurin kawar da ita da ake yi. A yanzu haka sama da sojoji dubu daya daga kasashen Nijar da Chadi suka nausa cikin Najeriya, kuma suna matukar samun nasara a yakin da suke da yan ta'addan. A gefe guda ita ma Najeriya yanzu ba a cika bada rahotanni tserewar da sojoji ke yi daga fagen daga ba kamar yadda aka saba gani a baya ba.

Nigeria Boko Haram Abubakar Shekau Archiv

Rikicin Boko Haram ya yi sanadin hallaka dubban mutane a arewacin Najeriya.

Masana dai na ganin cewar koma baya da kungiyar ta ke samu sakamakon luguden wutar da ake mata ne ya sanya ta yin mubayi'a ga kungiyar IS da su ke da akidu iri daya. Marc Engelhardt dan jarida da ke da kwarewa kan al'amuran Afirka ya ce "idan Abubakar Shekau ne ya fidda jawabin hadewa da IS, ya na son cimma wasu buruka ne, misali ya nuna cewa a yanzu ya na tare da kungiyar 'yan ta'adda mai karfi"

A baya dai Boko Haram ta nuna cewar ta na tare da Al-Qa'ida, yanzu kuma ta juya akalarta ga 'yan jihadi na IS. Wannan ya sanya mutane irinsu Manji Cheto mataimakin shugaban wata cibiyar tsaro a London da aka sani da Teneo Intelligence cewar "kashin Boko Haram ya fara bushewa bayan da makotan Najeriya suka hada kai don yakarta kuma kowa ya ga yadda kasashen ke murshe kungiyar. Wannan ya sanya kungiyar yanke shawarar neman mayaka daga wasu kasashe."

Symbolbild Islamischer Staat

Kungiyar IS na yunkurin kafa daular Islama a Iraki da kasar Siriya.Tuni da manazarta suka fara tofa albarkacin bakunansu kan irin riba ko akasin haka da suke ganin Boko Haram din za ta samu bisa yin mubayi'a ga kungiyar IS. Masanin harkokin 'yan ta'addan Afirka Marc Engelhardt ya ce "a kudu maso yammacin Libiya kungiyar IS na da sansani inda za a iya horar da 'yan Boko Haram. Wannan zai iya kasancewa in ma ba tuni an fara yin haka ba. A gefe guda kuma ana wucewa da bama-bamai ko kudi zuwa arewacin Najeriya domin kan iyakar ba ta da tsaro."

A cewar masanan dai kasashe irin su Jamhuriyar Najeriya su ne za su fi fiskatar matsala muddin ba murkushe kungiyar Boko Haram aka yi ba, inda ta arewa suke iyaka da 'yan ta'addan Mali da na Libiya, kana ga Boko Haram ta kudu kuma hadewar wadannan kungiyoyi na iya sa su yi karfi inda za su kawo illa babba ga zaman lafiya a yankin baki daya.

Sauti da bidiyo akan labarin