Yiwuwar fuskantar ′yunwa a Najeriya | Labarai | DW | 23.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yiwuwar fuskantar 'yunwa a Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai yiwuwar fuskanta ja'ibar 'yunwa a Arewacin Najeriya da Sudan ta Kudu da kuma kasar Yemen nan da watannin da ke tafe saboda halin da kasashen ke ciki na rashin zaman lafiya.

Shirin Samar da Abinci da kuma Shirin Abinci da Aikin Gona na Majalisar Dinkin Duniya ne suka ambata hakan cikin wani rahoto da suka fidda, inda suka ce abin da zai kara ta'azzara lamarin shi ne gaza kai kayan agaji a wuraren da sauyin yanayi da kuma koma-bayan tattalin arziki ya shafa. 

Rahoton da hukumomin biyu suka fidda ya nuna adadin wadanda wannan matsala ta 'yunwa za ta shafa a Najeriya inda ya ce yawan su zai haura miliyan guda daga nan zuwa watan Agustan da ke tafe.

A Sudan ta Kudu ma dai matsalar za ta shafi mutane sama da miliyan guda, inda rahoton ya ce da dama daga cikinsu za su kasance cikin tsananin bukatar abinci.