Yemen ta janye daga tebirin tattaunawa | Labarai | DW | 14.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yemen ta janye daga tebirin tattaunawa

Gwamnatin Yemen ta sanar da janyewa daga tebirin sulhu na zaman tattaunawar da take yi da wakillan 'yan tawayen Shi'a a Kuwait, a kokarin kawo karshen yakin da ke gudana a kasar.

Wani babban jami'in fadar Shugaba Abd Rabbo Mansur Hadi ne ya sanar da hakan, inda ya ce ba za su koma zagaye na biyu na zaman tattaunawar da za a soma a wannan Jumma'ar a kasar ta Kuwait ba, matsawar Majalisar Dinkin Duniya ba ta tilasta wa 'yan tawayen ficewa daga biranen kasar da suka hada da babban birnin kasar Sanaa ba, tare da mika makamansu. Kazalika ya ce sai Majalisar Dinkin Duniyar ta mayar da shugaban kasar kan kujerar mulkinsa kafin ya amince da duk wani batu na neman kafa gwamnatin rikon kwarya da za ta kunshi wakillan 'yan tawayen. Sai dai kuma Majalisar Dinkin Duniyar ba ta tabbatar da batun janyewar wakillan gwamnatin Yemen dindaga tattaunawar ba, wacce ta ce za a koma kanta ranar Jumma'a 15 ga wannan wata na Yuni da muke ciki kamar yadda aka tsara tun da farko.