Yemen: Annobar cutar kwalara ta yi kamari | Labarai | DW | 23.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yemen: Annobar cutar kwalara ta yi kamari

Sakamakon matsalolin kiwon lafiya da ake fuskanta a kasar Yemen, kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta Red Cross CICR ta yi hannunka mai sanda kan yadda annobar cutar kwalara ke dada kamari.

Kawo yanzu dai cutar ta kwalara ta yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu daya da 800 a cewar Kungiyar ta CICR wadda kuma ta ce idan ba a yi hattara ba adadin wadanda za su kamu da cutar a wannan shekara ta 2017 zai kai na mutane dubu 600. Bincike ya nunar cewa cikin mutane 45 na kasar mutun daya na dauke da cutar ta kwalara a cewar kungiyar agajin cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce hakan kuma ba komai ba ne illa sakamakon yake-yaken da ya lalata muhimman gine-ginen kasar tare da durkusar da tsarin kiwon lafiya baki daya.