Yayin da Musulmai ke bikin babbar Sallah an kai hari a Yemen | Labarai | DW | 24.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yayin da Musulmai ke bikin babbar Sallah an kai hari a Yemen

An karfafa matakan tsaro a kasashen Musulmai da dama saboda tsoron kai hari yayin da ake bukukuwa na Sallah.

A kasar Yemen wasu kunar bakin waken biyu sun kai hari masallacin 'yan tawayen Houthi da ke birnin Sanaa fadar gwamnatin kasar, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 25 sannan wasu masu yawa suka samu raunika, yayin da Musulmai ke bikin babbar Sallah.

A wannan Alhamis Musulmai a kasashen duniya ke bikin na Sallah bayan da jiya Laraba aka yi Hawan Arafat a Saudiyya da ke zama wani bangare mai mahimmci na aikin Hajji da Musulmai ke yi kana daya daga cikin rukunin addinin Islama. A bikin Sallah da ake yi a wannan Alhamis an karfafa matakan tsaro musamman a wuraren da ake samun tashe-tashen hankula daga tsageru masu kaifin kishin addinin Islama, kamar Najeriya da wasu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.