Yawan ′yan gudun hijirar Siriya na karuwa | Labarai | DW | 30.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yawan 'yan gudun hijirar Siriya na karuwa

Shugabar hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos ta ce nasarar da 'yan kungiyar nan ta IS ke samu a Siriya za ta sanya yawan 'yan gudun hijira sun karu.

Ms Amos ta shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar ta Dinkin Duniya cewar irin kutsa kai da mayakan IS din suka yi a arewacin Aleppo yanzu haka ya tilastawa kimanin mutane dubu 160 kauracewa matsugunansu, inda galibinsu suka gudu kasar Turkiyya don tsira da rayuwarsu.

Daga cikin wanda suka tserewa rikicin inji Amos mafi yawansu mata ne da kananan yara kuma halin da suke ciki na da tada hankali kana yanayin da aka shiga ya sanya kai kayan agaji gare na da matukar wahala.