1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawaitar kashe-kashe a Sudan ta Kudu

Mouhamadou Awal Balarabe
September 6, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da cin zarafin mata da kashe-kashen fararen hula da ake ci gaba da yi a tashin hankalin da ke gudana tsakanin Salva Kiir da Riek Machar a Sudan ta Kudu.

https://p.dw.com/p/4GTh1
Südsudan Verhandlungen zwischen Regierung und Opposition
Hoto: Reuters/J. Solomun

Wani rahoto da MDD ta fitar a wannan talata ya nunar da cewa kimanin fararen hula 173 ne aka kashe tare da yin garkuwa da 37 cikin watanni hudu a Sudan ta Kudu a fada da ke gudana tsakanin dakarun da ke biyayya ga shugaba Salva Kiir da mataimakin shugaban kasar Riek Machar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin ya shafi akalla kauyuka 28, kuma ya sa mutane kusan 44,000 tserewa daga kauyukansu. Sannan ta kara da cewa bangarorin  Salva Kiir da Riek Machar ne ke da alhakin take hakin bil-Adama da ke wakana a kasar.  

Tun bayan samun ‘yancin kai a shekara ta 2011 ne Sudan ta Kudu ke fama da rikice-rikice na siyasa da kabilanci, wanda ya hana ta murmurewa daga yakin basasar da ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 400,000 tare da raba miliyoyi da muhallinsu a tsakanin 2013 da 2018.