Yau take salla a Makka da Najeriya | Labarai | DW | 06.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yau take salla a Makka da Najeriya

Sallar ta bana a Saudiyya na zuwa a daidai lokacin da kasar ta shiga fargaba bayan wasu hare-hare a biranen Qatif da Riyad da Madina.

Beginn Pilgerfahrt Hadsch in Mekka 01.10.2014

Masallata a Masallacin Harami a Makka

Miliyoyin Musulmai a kasa mai tsarki ta Saudiyya da ma wasu kasashe kamar15 na Musulmi da ke zama Larabawa da wasu sassan duniya sun gudanar da sallar idi ta karamar salla a ranar Laraban nan.

A kasar Indonesiya da ke da yawan al'umma miliyan 250 da kuma ke zama kasar da tafi yawan mabiya addinin na Islama a duniya, miliyoyin wadannan al'umma ne suka fita sallar ta idi babban masallancin Al Azhar a Kudancin birnin Jakarta a ranar Laraba, da ke zama cikin kwanaki biyar da kasar ta ware na hutu duk da irin fargaba ta masu ikirarin Jihadi da ke kai hare-hare.

An dai tsara irin wannan ibada a wannan rana a wasu kasashen irinsu Bahrain da Masar da Jordan da Iraki da Najeriya da sauransu.