Yaro ya kai harin bam a Borno | Labarai | DW | 21.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaro ya kai harin bam a Borno

Wani yaro da shekarunsa ke tsakanin 10 zuwa 15 ya tada bam din da ke jikinsa a daren jiya a garin Banisheikh da ke jihar Borno a Najeriya.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasar Kanar Sani Usman Kukasheka ya fidda ta ce harin ya hallaka mutane 9 yayin da wasu da dama suka jikkata. 'Yan kungiyar nan ta kato da gora da ake kira Civilian JTF suka ne suka gano yaron da ma wasu yara biyu gabannin tada bam din daidai lokacin da suke bincike.

Rahotanni da ke fitowa daga inda wannan abin ya faru na cewar tuni aka kwashe gawarwakin wanda suka rasu yayin da aka garzaya da wanda suka jikkata zuwa asibiti don yi musu magani. Jami'an tsaro yanzu haka sun tsaurara matakan tsaro a garin na Banisheikh da kewayensa domin magance sake faruwar irin wannan lamari.