Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Gaza | Labarai | DW | 26.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Gaza

Ayau ne yarjejeniyar nan ta tsagaita wuta ya fara aiki,a inda sojin sakai na palasdinu zasu daina kai harin rokoki kann yankunan Izraela,ayayinda a nata bangare dakarunta zasu daina kutse da sukeyi a yankin cin gashin kann Palasdibnawan.Sojojin Izraelan dai sun sanar da fara janye dakarunsu daga Zirin Gazan tun a daren jiya,gabannin fara aiwatar da wannan yarjejeniya a yau.Shaidu daga yankin Palasdinawan dai sun tabbatar dacewa dakarun Izraelan sun tattara komatsansu sun fice daga arewacin Gazan tun a daren jiya,yankin da mayakan suka mamaye cikin makonni da suka gabata.Sake aiwatar da wannan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu da aka cimma tun a bara dai,zai iya taimaka wajen sharan fagen taron hadin gwiwa da ajima a dakonsa,tsakanin shugaban Palasdinawa Mahamoud Abbas da Premiern Izraela Ehud Olmert,adangane da samar da zaman lafiya a yankin na gabas ta tsakiya.