Yarjejeniyar sulhu tsakanin alúmomin Somalia | Labarai | DW | 17.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar sulhu tsakanin alúmomin Somalia

Shugabanin gwamnatin riƙon ƙwaryar Somalia mai samun tallafi daga Habasha sun cimma sanya hannu akan yarjejeniyar sulhu bayan taron sasantawa ta haɗin kan kasa da aka gudanar wanda baá kammala shi ba a watan da ya gabata. A ranar lahadin nan ne aka sanya hannu akan yarjejeniyar a ƙasar Saudiya bisa tsoma baki na sarki Abdalla wanda ya ɗokanta ga samun kwanciyar hankali a ƙasar Somalian. Bá sami cikakken bayanai a game da ƙudirorin da yarjejeniyar ta ƙunsa ba. An tashi taron sulhun da aka gudanar a Somalia ba tare da cimma wata madafa ba, abin da ya sanya jakadu na ƙasashen ƙetare buƙatar faɗaɗa wakilcin taron domin kawo ƙarshen rikicin ƙasar wanda ya samo asali tun bayan da aka hamɓarar da gwamnatin Mohammed Siad Bare a shekarar 1991. Shugaba Abdullahi Yusuf da P/M Ali Mohammed Gedi da kakakin majalisar dokoki Sheikh Aden Mohammed Nur na daga cikin waɗanda suka halarci taron na Saudiya. Ƙasar saudiyan ta yi kira ga dukkan bangarorin sun martaba yarjejeniyar da suka sanyawa hannu.