1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar sulhu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Pinado Abdu WabaFebruary 5, 2015

Bangarorin da ke gaba da juna a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta sai dai an yi babu gwamnatin Samba-Panza

https://p.dw.com/p/1EWHq
Catherine Samba-Panza 2014 Präsident Zentralafrikanische Republik
Hoto: J. Richards/AFP/Getty Images

Dan asalin Kenyan da ke shiga tsakani a tattaunawar sulhun Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya fadawa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa wakilan bangarorin da ke gaba da juna sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Mai shiga tsakani Kenneth Marende ya fadawa manema labarai cewa tsoffin 'yan Seleka da anti Balaka sun amince su daina sanya kananan yara aikin soji su kuma daina kai hari kan fararen hula.

Kenya ta shiga gaba wajen jagorantar tattaunawar sulhu a Jamhuriyar Afirka Ta tsakiya bayan ta sami hadin kan Kungiyar Tarayyar Afirka, sai dai da yawa na shakkun sahihancin tattaunawar tunda dai ba yi shi tare da hadin kan gwamnatin shugabar kasa Catherine Samba-Panza ba kuma ma yarjeniyoyin tsagaita wutan da aka kulla a baya da wakilan bangarorin ba su dore ba