Yarjejeniyar samar da ruwa tsakanin ƙasashe uku a Yankin Gabas ta Tsakiya | Zamantakewa | DW | 11.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yarjejeniyar samar da ruwa tsakanin ƙasashe uku a Yankin Gabas ta Tsakiya

Yarjejeniyar za ta share hanyar fara aiwatar da wani katafaren aikin farfaɗo da kogin Jordan da ya fara ƙafewa, ta hanyar haɗe shi da Tekun Bahar Maliya

Ƙasashen Jordan da Isra'ila da Falasɗinu sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar aiwatar da shirin haɗe Tekun Bahar Maliya da kogin Jordan, don cin moriyar ruwan kogunan tsakaninsu.Rattaɓa hannu kan wannan yarjejeniya da ministocin albarkatun ruwa na ƙasashen uku suka yi, a cibiyar bankin duniya da ke birnin Washington na Amirka, zai share hanyar fara aiwatar da wani katafaren aikin farfaɗo da kogin Jordan da ya fara ƙafewa, ta hanyar haɗe shi da Tekun Bahar Maliya Yadda shirin ya tanadi gina matatar ruwan gishiri a garin Aqaba na Jordan, wanda za a dinga tace ruwan tekun a cikinta, kafin daga baya a rarraba wa kasashen uku da suka rattaɓa hannu a kan yarjejeniyar. Hazim Nasir, ministan albarkatun ruwa na ƙasar ta Jordan, ya ce yarjejeniyar wadda za ta rage matsalar ƙarancin ruwan a ƙasahen, somin taɓi ne na ƙarfafa zaman cuɗe ni- in -cuɗe-ka tsakanin ƙasashen yankin;

"Mun yi haɗin gwiwa da takwarorinmu da ke wannan yanki,don aiwatar da wannan shirin da zai taimaki al,umominmu baki ɗaya,kuma zai share hanyar tabbatar da zaman lafiya tsakanin ƙasashen da ba sa ga maciji da juna."

Fluss Jordan

Kogin Jordan

Ƙasar Isra'ila, ta ce a ta bakin ministanta, na makamashi, Silvan Shalom, ɓurin iyaye da kakkannin da suka kafa ƙasar bani yahudu suka jima suna mafarkinsa ya cika da cimma wannnan yarjejeniya. Al'ummar Falasɗinawa da ke kokawa da daddatse musu hanyoyin ruwa da Isra'ila ke yi, sun nuna takaicinsu da yarjejeniyar da suke cewa za ta daɗaɗa wa Isra'ila ne kaɗai, kasantuwar Isra'ila ce kaɗai ke da iko da gaɓar kogin Jordan."Hukumar kwarya-kwaryar gashin kan Palasɗinawa ba da da wata katabus kan wannnan shiri.Domin kasashen da ke da cikakken iko cin gashin kai,su ked a ikon yin tasarrufi kan goguna da tekunan duniya."Ita kuwa ƙungiyar Hamas ta Palalsɗinawa, Allah wadai ta yi da yarjejeniyar da ta ce, za ta halatta wa Isra'ila ruwan da yake mallakar Falasɗinawa ne.Masu fafutukar kare mahalli da yanayi a ƙasar Jordan sun fito fili sun bayyana adawarsu da shirin gina matatar ruwan gishirin teku a ƙasar, yadda suka ce, hakan zai yi wa mahalli illa.Ƙasar Isra'ila dai, wacce ta fi iko da yankuna mafi girma na koguna ta ƙi amincewa a gina matattar a ƙasarta, don miƙa wuya bori ya hau ga buƙatun ƙungiyoyin kare mahalli.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Pinaɗo Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin