1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar kasuwanci ta EU da Afirka

March 28, 2014

Kasashen Turai za su cire wa takwarorinsu na yammacin Afirka kudin fito na kayayyaki, tare da bude kasuwanninsu ga juna a karkashin yarjejeniyar da za su sa hannu a kanta.

https://p.dw.com/p/1BXax
Deutschland Steuereinnahmen Banknoten
Hoto: picture-alliance/dpa

Kasashen Afirka ta yamma sun gudanar da wani taro a jiya Alhamis tsakaninsu da kungiyar tarayyar Turai ta EU a mastayin sharar fage na cimma wasu jerin yarjejeniyoyi da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin bangarorin biyu.

Wannan tattaunawa dai ta samo asalinta kimanin shekaru goman da suka gabata, ta fuskanci tsaiko saboda rashin fahimtar juna da aka rika samu tsakanin bangarorin biyu, to sai dai a karshen makon nan ne za a kai ga sanya hannu kan yarjejeniyar.

Daga cikin irin abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa dai sun hada da cire kudin fito na kayayyaki tsakanin kasashen na yammacin Afirka da Turai kazalika Turai za ta bude kasuwanninta ga 'yan nahiyar yayin da suma za su yi hakan ga kasashen na EU.

Tuni dai masana tattalin arziki suka ce lamarin zai taimakawa 'yan kasuwa da ma dai bunkasa tattalin arziki na wannan yanki na Afirka wanda yawan al'ummarta ya tasamma miliyan 300.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe