Yarjejeniya tsakanin Iran da IAEA | Labarai | DW | 11.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniya tsakanin Iran da IAEA

Kasar Iran ta amince jami'an hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA sun bincika tashoshinta da ake ganin za ta iya amfani da su wajen kera makamin kare dangi.

Hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta cimma yarjejeniya da Iran a kan shirinta na inganta wannan makamashi da ake takaddama akai. Babban jami'in da ke kula da harkokin nukiliya na Iran Ali Akbar Salehi ne ya yi wannan sanarwa a birnin Teheran, bayan da ya rattaba hannu akan yarjejeniya da shugaban IAEA Yukiya Amano.

Sassa biyu sun amince jami'an IAEA sun rika bincika daukacin cibiyoyin nukiliyar da Iran ta mallaka, ciki kuwa har da na Parchin da ke cikin yankin kudu masu gabashin kasar. Hukumomin leken asiri na kasashen Turai suna zargin Iran ta neman amfani da wannan tashar wajen kera makamin kare dangi.

Da farko dai Iran da sauran kasashen nan biyar da ke da kujarar din-din-din a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Jamus sun watse a taronsu ba tare da cimma matsaya ba a birnin Jeniva.

Sai dai kuma wannan birni zai dauki bakwancin wani sabon zaman tattaunawa tsakanin manyan kasashen duniya da kuma Iran a ranar 20 ga wannan wata na Nowamba idan Allah ya kaimu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu