Yarjejeniya tsakanin Afirka ta Kudu da Francois Bozize | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 05.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Yarjejeniya tsakanin Afirka ta Kudu da Francois Bozize

Tun a shekarar 2007 aka kulla yarjejeniyar game da girke dakarun Afirka ta Kudu a kasar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sannan aka sabunta ta a bara.

A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. A babban labarinta jaridar die Tageszeitung ta fara ne da cewa.

„Bayan bankado wasu harkokin kasuwanci tsakanin Afirka ta Kudu da hambararren shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Francois Bozize, an yi tofin Allah tsine da manufofin ketare na jam'iyar ANC gabanin wani taron kolin shugabannin yankin da ya gudana a birnin N'djamena na kasar Chadi. Neman karin haske game da rawar da Afirka ta Kudu ta taka a Afirka ta Tsakiya ya kamata ya mamaye zauren taron. A hukumance Afirka ta Kudu dai ta yi asarar sojoji 13 a fafatawa da ‚yan tawayen Seleka, amma ‚yan Seleka sun ce sojojin Afirka ta Kudu 35 suka kwanta dama. Tun bayan sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin kasashen biyu a shekarar 2007 dakarun Afirka ta Kudu ke Bangui, sannan a karshen shekarar 2012 ta tura karin sojoji dake horas da takwarorinsu na Afirka ta Tsakiya. ‚Yan adawa sun zargi gwamnatin shugaba Jacob Zuma da yaudarar jama'a. Kasar dai na gudanar da aikace aikace musamman a bangaren hako ma'adanan karkashin kasa, a saboda haka ne ake zargin cewa ta tura sojojinta kasar ta Afirka ta Tsakiya ne don kare muradunta na tattalin arziki.“

Partisans of new Central African Republic leader Michel Djotodia hold flags and banners during a support march in the streets of Bangui on March 30, 2013. The Central African Republic's new strongman Michel Djotodia vowed Saturday not to contest 2016 polls and hand over power at the end of the three-year transition he declared after his coup a week ago. (banner reads; 5th districj, Banda-GB quarter, Yes to change, Support the President Michel Djotodia Am Nondroko '). AFP PHOTO / SIA KAMBOU (Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)

Zanga-zangar goyon bayan sabbin mahukuntan birnin Bangui

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung tsokaci ta yi a kan taron kolin shugabannin a birnin N'djamenan Chadi a kann juyin mulkin na Bangui da cewa taro ne na rufa-rufa.

Taron kare kai a birnin N'djamena

„Shugabannin kasashen yankin Tsakiyar Afirka da shugaban Afirka ta Kudu sun tattauna game da juyin mulkin da Seleka ta yi a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya to sai dai bayan jadawalin taron a hukumance, wannan haduwar ba komai ba ne illa wani yunkurin kare kai da kuma muradunsu. Tun wasu ‚yan shekaru da suka wuce, taron kolin kungiyoyin yankuna a Afirka bayan wani juyin mulki da yayi nasara, ya zama tamkar wata al'ada. Wani kudurin kungiyar tarayyar Afirka a shekarar 2007 game da demokradiyya, zabe da kuma tafiyar da gwamnati, ya yi tir da karbe mulki da karfin tuwo. Kudurin ya tanadi mayar da irin wannan gwamnati saniyar ware a cikin AU tare da daukar matakan jan kunnen masu hannu. A makon daya gabata AU ta sanya takunkumi a kan Michell Djotodia da mukarrabansa. Sai dai daukacin shugabannin da suka hadu a Ndjamena ba su da wata kyakkyawar shaida ta tafiyar da mulkin demokradiyya. Saboda haka ba bu wani mataki na a zo a gani da za su iya dauka kan sabbin hukumomin na Bangui.“

Alamun samun sauyi mai ma'ana a Sudan

Shugaban Sudan ya sako firsinonin siyasa abin da ya karfafa fatan samun canji inji jaridar Süddeutsche Zeitung.

Political prisoners walk out after their release from Kober Prison in Khartoum April 2, 2013. Sudan's President Omar Hassan al-Bashir on Monday ordered the release of all political prisoners, a move cautiously welcomed by the opposition in the tightly-controlled African country. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah (SUDAN - Tags: POLITICS CRIME LAW)

Tuni an fara sako wasu firsinonin siyasa a Sudan

„Idan wani shugaban kama karya a Afirka ya ba da sanarwar cewa kasarsa na bukatar sabbin jini, ba safai hakan ke samun karbuwa ba. Amma bisa ga dukkan alamu a wannan karon da gaske shugaban ya ke, domin ya ce ba zai sake tsayawa takara a zaben shekarar 2015 ba. Duk da cewa ba a san abubuwan dake boye ba, amma wasu daga cikin shugabannin 'yan adawa sun yaba da alkawarin yin afuwar da shugaba Omar al-Bashir ya yi da cewa wani albishir ne dake kan turbar samar da kyakyawan ci-gaba a kasar ta Sudan."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe