Yarjejeniya a fannin shari′a tsakanin kasashe uku na Sahel | Labarai | DW | 11.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniya a fannin shari'a tsakanin kasashe uku na Sahel

Kasashen Mali, Chadi da Jamhuriyar Nijar da suke fama da hare-haren 'yan ta'adda, sun cimma wata yarjejeniya ta hulda a fannin shari'a domin inganta yaki da ta'addanci.

Symbolbild Afrika Sicherheit im Sahel (Pascal Guyot/AFP/Getty Images)

Yaki da ta'addanci a tsakanin kasashen Sahel

Da yake magana kan yarjejeniyar, ministan shari'a na kasar Chadi Mahamat Hassan, ya ce bisa tsarin da suka cimma, a shari'ance babu iyaka tsakanin Chadi, Nijar da kuma kasar Mali, inda ya ce hakan zai bada damar inganta yakin da suke da 'yan ta'adda da ke fakewa a tsakanin kasashen uku. Daga nashi bangare ministan shari'a na Jamhuriyar Nijar Marou Amadou, ya ce cimma wannan yarjejeniya ya zo ne a daidai lokacin da kasashen uku ke fusknatar matsaloli na 'yan ta'adda, da masu safarar muyagun kwayoyi, da ma safarar mutane.

Kasashen uku na Nijar, Mali da kuma Chadi, za su yi hulda hannu da hannu tare da aiwatar da bincike na hadin gwiwa da ma batun tisa keyar masu laifi daga wannan kasa zuwa wanccan, a wani mataki na kauce wa wani dogon turanci da ake fuskanta a fannin shari'a da ke sanya dabaibayi wajen magance tarin matsaloli na yaki da ta'addanci.