Yarinya ta 3 ta rasa ranta sakamakon zazzabin murar tsuntsaye a Turkiya | Labarai | DW | 06.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarinya ta 3 ta rasa ranta sakamakon zazzabin murar tsuntsaye a Turkiya

Rahotanni daga kasar Turkiya sun nuna cewa a yau wata yarinya yar shekaru 15 ta uku ta rasa ranta sakamakon zazzabin murar tsunyaye da ya kashe yan uwanta biyu cikin mako guda,yayinda kwayar cutar da ta kashe mutane 74 a Sin da kudu maso gabashin Asiya take shigowa Turai.

Yanzu haka likitoci sunce fiye da mutane 20 ne yawancinsu yara,ake binciken lafiyarsu ko suna dauke da wannan kwayar cuta a asibitin da wadannan yara suka rasu.

Wadannan yara Hulya Mehmet Ali da Fatma da suka fito daga gida daya suna zaune ne a wani kauye dake gabashin Turkiya kusa da bakin iyaka kasar da Armenia da kuma Iran.

A halin da ake ciki kuma likitoci sun fara binciken gano ko cutar tana yaduwa tsakanin mutum da mutum ko kuwa ta hanyar gogaiya da kaji ne kadai.