Yara ƙanana kusan 300 aka kashe a Gaza | Labarai | DW | 02.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yara ƙanana kusan 300 aka kashe a Gaza

Dakarun Isra'ila na ci gaba da ruwan bama-bamai a Gaza a faɗan da a yau aka shiga cikin kwanaki na 25.

Hare-haren dai sun fi muni ne a yankin kudancin Gaza, inda Isra'ila ke neman sojinta guda da ya ɓace tun a jiya Jumma'a. Isra'ila dai na zargin Hamas da sace sojin, zargin da Hamas ta ƙaryata.

Mazauna garin Rafa dai sun bayyana cewar suna cikin halin matsi inda wasu suka ce sojojin Isra'ilan sun gargaɗesu da ka da su tsere daga yankin. Sama da bama- bamai 200 ne dakarun na Isra'ila suka jefa a wannan ranar, ɗaya daga cikin muhimman wuraren da suka lalata shi ne jami'ar musulunci ta Falasɗinu da ke Gazan, inda suke zargi ana ƙera makamai a ciki.

A yanzu haka dai tawagar jami'an Falasɗinu daga Ramallah da shugabannin da ke gudun hijira na kan hanyarsu ta zuwa birnin Alƙahirar Masar. Sai dai majiyar Isra'ila na nuni da cewar, ba za ta tura tawagarta ba.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdourrahman Hassane