′Yar kare hakkin masu hakar ma′adanai a Afirka ta Kudu | Himma dai Matasa | DW | 19.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

'Yar kare hakkin masu hakar ma'adanai a Afirka ta Kudu

Marie-Jane Matsolo wata matashiya yar gwagwarmaya a Afirka ta kudu ta shiga gaba domin kwato hakkin masu tonar ma'adanai musamman wadanda suka gamu da rashin lafiya har iya tsawon rayuwarsu.

Ma'aikata masu hakar ma'adanai sun gudanar da zanga-zanga a saman titunan birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu a karkashin jagorancin Mary-Jane Matsolo, domin kwato hakkin masu hakar ma'adanai da suka gamu da rashin lafiya har iya tsawon rayuwarsu. Irin wannan na cikin abubuwa masu muhimmanci ga rayuwarta karkashin Kungiyar Treatment Action Campaign da ke neman inganta lafiyar 'yan kasa:

"Muna da matukar kwarewa kan abubuwa da suka shafi adalci tsakanin al'uma da lamuran da suka shafi lafiya cikin kasar Afirka ta Kudu."

Kungiyar Treatment Action Campaign ta gwagwarmaya ta fara fitowa a kasar Afirka ta Kudu sakamakon matakan da ta dauka kan shawo kan cutar AIDS/SIDA tare da samar da magunguna domin kai wa ga mutane masu yawa. Marie-Jane Matsolo tana aiki na dogon lokaci kusa da wani chuci take aiki, inda ta mayar wajen na baje hotunan ma'aikata marasa lafiya da rubuce-rubucen neman tabbatar da adalci.

 

Matashiyar tana bayar da taimako ga dubban masu hakar ma'adanai wadanda suka kamu da cututtuka na nunfashi a wuraren tono ma'adanai da suka yi suna a Afirka ta Kudu. Kuma lokacin zanga-zanga ta nuna matukar farin ciki sakamakon gamuwa da Ricahrd Spoor lauyan da ya yi suna wajen kare hakkin dan Adam, wanda yake wakiltar kimanin ma'aikata dubu-30 a kotu wadanda suke rashin lafiya. Sannan ya nuna jin dadi da irin aikin na Marie-Jane Matsolo yana mai cewa:


"Muna bukatar samun kungiyoyi masu zaman kansu da za su wayar da kan mutane, tare da zama wani bangare na siyasa domin magana da sunan mutane."

A nata bangaren Marie-Jane Matsolo ta ce tilas a tuna da makomar masu hakar ma'adanai:


"Wadannan mutane sun mika rayuwarsu ga ci-gaba da tattalin arziki abin da ya amfani mutane masu yawa da kamfanonin hakar ma'adanai. Amma yau suna mutuwa cikin takaici. Wannan ba daidai ba ne."

Ita dai Marie-Jane Matsolo matashiyar 'yar gwagwarmaya ta kan tuna mahaifinta wanda ya rasu shekaru biyu da suka gabata saboda wakokin gwagwarmaya da yake rubutawa domin tabbatar da gaskiya da adalci, kuma nuna kiyayya ga mulkin nuna wariyar launin fata da aka yi a Afirka ta Kudu.